Laraba 6 Mayu 2026 - 22:28
Silsilar Tattaunawa Kan Mahdawiyya (22) | Yanayin Mulkin Imam Mahdi (AS)

Hauza/ Yanayin mulkin Imam Mahdi (AS) yana daidai da yanayin na Manzon Allah (SAWA). Kamar yadda Manzon Allah (SAWA) ya yi yaƙi da jahiliyya a zamaninsa kuma ya kafa addinin Musulunci na gaskiya wanda ke tabbatar da sa’adar duniya da lahira, haka nan Imam Mahdi (AS) zai fito ya yi yaƙi da jahiliyya ta zamani, wacce ta fi wadda ta gabata muni, ya kuma gina ƙimar addini da na Allah a kan ragowar jahiliyyar zamani.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito, jerin batutuwan Mahdawiyya da ake gabatarwa da taken “Zuwa ga Al’umma Mai Manufa”, an shirya su ne domin yaɗa koyarwa da ilimin da suka shafi Imam Mahdi (AJ), kuma ana gabatar da su ga masu ilimi da masu sha’awar wannan fanni.

Yanayin Mulkin Imam Mahdi (AS)

Kowane mai mulki yana da salon nasa gudanarwa. Lokacin da Imam Mahdi (AS) ya zama shugaba na duniya, zai yi amfani da nasa tsarin na musamman. Hadisai sun bayyana cewa salon Imam Mahdi (AJ) daidai yake da salon Manzon Allah (SAWA).

Imam Sadiƙ (AS) ya ce:

 «يَصْنَعُ كَمَا صَنَعَ رَسُولُ اللَّهِ ﷺ، يَهْدِمُ مَا كَانَ قَبْلَهُ كَمَا هَدَمَ رَسُولُ اللَّهِ ﷺ أَمْرَ الْجَاهِلِيَّةِ، وَيَسْتَأْنِفُ الْإِسْلَامَ جَدِيدًا». 

(Imam Mahdi) zai aikata kamar yadda Manzon Allah (SAWA) ya aikata; zai rushe abin da ke kafin zuwansa kamar yadda Manzon Allah ya rushe tsarin jahiliyya, sannan zai kafa Musulunci a sabuwar hanya. (Al‑Ghaybah Nu’umani, juzu’i na 1, shafi na 230)

Wato Imam Mahdi (AJ) zai sake farfado da Musulunci da gaskiya da tsabta, ya kawar da duk abin da jahiliyyar zamani ta gina.

 Salon Jihadi da Yaƙin Imam Mahdi (AJ)

Imam Mahdi (a.s.) zai jagoranci juyin juya halin duniya, ya kawar da kafirci da shirka, ya kuma gayyaci mutane zuwa ga addinin Musulunci.

Manzon Allah (SAWA) ya ce:

«سُنَّتُهُ سُنَّتِي، يُقِيمُ النَّاسَ عَلَى مِلَّتِي وَشَرِيعَتِي».

Sunnarsa sunnata ce; zai sa mutane su bi addinina da shari’ata. (Kamal al‑Din, juzu’i na 2, shafi na 411)

Haka kuma Imam Baƙir (AS) ya ce:

«يَسْتَخْرِجُ التَّوْرَاةَ وَسَائِرَ كُتُبِ اللَّهِ مِنْ غَارٍ بِأَنْطَاكِيَةَ، فَيَحْكُمُ بَيْنَ أَهْلِ التَّوْرَاةِ بِالتَّوْرَاةِ، وَبَيْنَ أَهْلِ الْإِنْجِيلِ بِالْإِنْجِيلِ، وَبَيْنَ أَهْلِ الزَّبُورِ بِالزَّبُورِ، وَبَيْنَ أَهْلِ الْقُرْآنِ بِالْقُرْآنِ».

"Zai fito da Attaura da sauran littattafan Allah daga kogon Antakiyya, sannan zai yi hukunci da Attaura ga masu bin Attaura, da Injila ga masu bin Injila, da Zabura ga masu bin Zabura, da Alƙur’ani ga masu bin Alƙur’ani. (Al‑Ghaybah Nu’umani, shafi na 237)

-Salon Shari’ar Imam Mahdi (AS)

Imam Mahdi (AJ) wanda Allah ya tanada don kafa adalci a duniya, zai yi hukunci da cikakken adalci kamar yadda Imam Ali (AS) ya yi.

Manzon Allah (SAWA) ya ce:

 «إِذَا قَامَ الْقَائِمُ حَكَمَ بِحُكْمِ دَاوُدَ وَسُلَيْمَانَ، لَا يَسْأَلُ الْبَيِّنَةَ».

"Lokacin da Qa'im (Mahdi) ya tashi da tutarsa, zai yi hukunci kamar Annabi Dawuda da Annabi Sulaiman; ba zai nemi shaida daga mutane ba." (Bihar al‑Anwar, juzu’i na 52, shafi na 320)

Salon Gudanarwar Mulkin Imam Mahdi (AS)

Shugabanni masu gaskiya su ne ginshiƙan mulkin adalci.

Manzon Allah (SAWA) ya ce:

 «عَلَامَةُ الْمَهْدِيِّ أَنْ يَكُونَ شَدِيدًا عَلَى الْعُمَّالِ، جَوَادًا بِالْمَالِ، رَحِيمًا بِالْمَسَاكِينِ».

"Alamar Mahdi ita ce: zai kasance mai tsauri ga ma’aikata, mai kyauta da dukiya, kuma mai tausayi ga talakawa." (Mu’ujam Ahadith al‑Imam al‑Mahdi, juzu’i  na 1, shafi na 246)

Salon Tattalin Arzikin Imam Mahdi (AS)

Imam Mahdi (AS) zai kafa tsarin tattalin arziki na adalci, inda dukiyar jama’a za ta rabu daidai.

Manzon Allah (SAWA) ya ce:

«إِذَا خَرَجَ مَهْدِيُّنَا ذَهَبَتِ الشَّحْنَاءُ وَالْعَدَاوَةُ، وَرُفِعَ الظُّلْمُ».

"Lokacin da Mahdinmu ya fito, gaba da ƙiyayya za su gushe, kuma zalunci zai ƙare. (Bihar al‑Anwar, juzu’i na 52, shafi na 309)

Haka kuma Manzon Allah (SAWA) ya ce:

«يَكُونُ فِي آخِرِ أُمَّتِي خَلِيفَةٌ يَحْثُو الْمَالَ حَثْيًا».

A ƙarshen al’ummata za a sami khalifa wanda zai raba dukiya sosai. (Mu’ujam Ahadith al‑Imam al‑Mahdi, juzu’i na 1, shafi na 232)

Salon Rayuwar Imam Mahdi (AJ)

Rayuwar Imam Mahdi (AS) za ta kasance mai cike da tawali’u da tsoron Allah, kamar rayuwar Imam Ali (AS).

Imam Sadiq (AS) ya ce:

«وَاللَّهِ مَا لِبَاسُهُ إِلَّا الْغَلِيظُ، وَمَا طَعَامُهُ إِلَّا الْجَشِبُ».

"Na rantse da Allah, tufafinsa za su kasance masu kauri, abincinsa kuma mai sauƙi da tsauri. (Al‑Ghaybah Sheikh Tusi, juzu’i na 1, shafi na 459)

Haka kuma ya ce:

«اِنَّ قائِمَنا اِذا قامَ لَبِسَ لِباسَ عَلِی وَ سارَ بِسیرَتِهِ.»

“Lokacin da Mahdinmu ya fito, zai sa tufafin Ali (AS) kuma zai yi tafiya bisa salon sa.” (Wasa’il al‑Shi’a, juzu’i na 5, shafi na 17)

Wannan tattaunawa za ta ci gaba...

An tsakuro daga littafin"Negine Afarinesh" da ɗan gyara kadan.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha